Rikicin Gaza na cigaba da ta'azara
July 22, 2014A yayin da jami'an diplomasiyya ke yunkurin dakile rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya, lamura a zirin Gaza na cigaba da ta'azara, ko a yau sai da sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya yi godo da Falasdinu da su amince da yarjejejniyar tsagaita wuta
"Hamas na da shawarar da zata yanke mai mahimmancin gaske domin zai yi tasiri kan mutanen da ke rayuwa a Zirin Gaza, kuma Misrawa sun bayar da damar zuwa teburin tattaunawa domin tattaunawa da kowane bangare".
Bayan da ya gana da Sakataren harkokin wajen Amirkan John Kerry a birnin Alkahira, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya karasa Isra'ila inda ya gana da Firaminista Benjamin Netanyahu domin shi ma ya ba da hadin kan shi wajen kawo karshen rikicin na tsawon makonni biyu yanzu inda ya shawarci bangarorin kamar haka
"Sako na ga Isra'ila da Falasdinu guda ne. Ku daina fada, ku fara tattaunawa, kuma ku mayar da hankali kan ummul abaisin wannan rikicin domin kada mu sake dawowa kan wannan batun a tsukin watanni shidda ko kuma shekara guda domin wajibi ne mu yi la'akari da abubuwan da suka fi ci mana tuwo a kwarya a kuma mutunta hakkin dan adam"
Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar