Hamas da Isra'ila rikici ya balle
August 9, 2018An dai rika jin karar jiniyar jami'an tsaro a yankin kudancin Isra'ila da faduwar ranar Laraba inda jami'an tsaro suka yi gargadi ga jama'a da su janye jiki su nemi mafaka a gidajensu bayan da aka ga makaman roka kimanin 80 na Hamas sun afka yankin, sojan na Isra'ila su ma suka mayar da martani da kai hare-hare sau 140 kusa da yankin na Hamas a Zirin Gaza.
Wannan barkewar fadan dai na zuwa ne yayin da Majalisar Dinkin Duniya da kasar Masar ke kokarin ganin an kai ga cimma wata matsaya da za ta kawo karshen watanni da aka dauka ana tashin hankali tsakanin bangarorin biyu.
Kafafen yada labarai dai na Isra'ila sun nunar da cewa Yahudawa a yankin Sderot da wasu garuruwa da ke kusa da iyaka sun samu raunuka yayin da a Gaza aka bayyana mutuwar mutum guda baya ga wadanda suka samu rauni.