Rikicin Isra'ila da Falasdinu
April 15, 2012Isra'ila na amfani da daruruwan 'yan sanda wajen dakatar da wasu masu zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinu zuwa gabar yamma da tekun Jordan. A filin jirgin saman Ben Gurion da ke birnin Tel Aviv, yan sandan sun gudanar da bincike kan wasu daga cikin masu boren da suka isa, suka kuma bide su da su koma gida. Tun farko dai wasu jiragen saman suka soke sauka a Israilan sakamakon matsin kaimin da mahukuntan suka yi masu, bayan da suka sami labarin cewa zasu yi jigilar wasu sanannun masu fafutuka 100 a jiragen nasu. Kimanin mutane 1, 500 suka nuna sha'awan kasancewa a zanga-zangar ta bana wacce ake ma taken "Maraba Falasdinu" wacce kuma aka saba gudanarwa kowace shekara a yankin yamma da gabar tekun Jordan. Kuma makusudin wannan zanga-zanga shine nuna adawa da irin matakai masu tsaurin da Israilan ta ke amfani da su wajen jagorantar yankunan Falasdinu.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Usman Shehu Usman