1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hallaka mutane da dama a yankin Darfur

Abdoulaye Mamane Amadou
January 2, 2020

Akalla mutane 50 ne suka hallaka wasu fiye da 240 suka jikkata sakamakon kwanaki biyun da aka shafe a na rikin kabilanci a yankin yammacin Darfur na kasar Sudan.

https://p.dw.com/p/3VePq
Sudan Khartoum Feuer in Fabrik
Hoto: Reuters/M. Mohamed

Rahotanni sun ce rikicin ya barke a tsakanin 'yan kabilun larabawan yankin inda dauke da bindigogi mutanen suka yi ta harbin juna da kukkona gidajen jama'a lamarin da ya kara kazancewar adadin wadanada suka jikkata.

Hukumomin kasar ta Sudan sun kakaba dokar tabaci a yankin, kana kuma tuni wata tawagar ta musamman ta hukumomin kasar ta isa a birnin El Geneina, inda aka kara karfafa matakan tsaro.