1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Darfur: Rikicin kabilanci na daukar sabon salo

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
April 5, 2021

Akalla mutane 18 ne suka hallaka wasu kuma 54 suka jikkata biyo bayan barkewar fadan kabilanci a yankin El-Geneina, na yammacin Darfur na kasar Sudan.

https://p.dw.com/p/3rbQi
Südsudan UN-Mission (UNAMID) in Darfur
Hoto: Getty Images/AFP/A. Shazly

Wannan dai shi ne kashe-kashe mafi muni da ya auku a baya-bayan nan a yankin da ke yammacin Sudan mai fama da tashe-tashen hankula, a cewar hukumomin kula da lafiyar al'ummar kasar.

Sai dai a wata sanarwar da suka fitar, hukumomin lafiyar Sudan sun sheda cewa galibin wadanda suka jikkata, sun karbi magani ne a babban asibitin jami'ar El-Geneina da ke lardin Darfur.