1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kan iyaka tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu

February 3, 2013

Tun bayan kasashen suka raba gari a shekara ta 2011,kawo yanzu yanzu dai rikici ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin kasashen biyu a kan iyakoki.

https://p.dw.com/p/17XOd
Hoto: KHALED DESOUKI/AFP/Getty Images

Fadar gwamnatinJuba,ta zargi dakarun kasar Sudan ta Kudu da kai hare hare a yankunan kasarta inda jiragen yaki suka yi aman wuta a kan wani ayarin motocin sojin Sudan ta Kudu inda daya daga cikin sojojin ya rasa ransa.,yayin da wasu hudu suka jikata.
To saidai kamar kullum a duk lokacin da hakan ta faru,gwamnatin Khartum,ta yi watsi da zargin. Tun lokacin da kasar sudan ta balle daga kasar Sudan ana yawan samun rikici tsakanin kasashen biyu musamman a kan arzikin man fetur da Allah ya huwacewa yankin da ake takaddama a kanshi.
Ko a cikin watan Janairun nan an gudanar da wasu tautaunawa tsakanin magambatan kasashen biyu a birnin Adis Abbaba na kasar Habasha ba tare da an cimma wani daidaito ba.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Halima Balaraba Abbas