1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Kwango na ci gaba da kamari

July 8, 2022

Kwanaki bayan ganawa tsakanin shugabannin Kwango da na Ruwanda, hare-hare na kara ta'azzara a wasu sassan Kwango, lamarin da ya jefa fararen hula cikin mawuyacin hali.

https://p.dw.com/p/4DsQ5
Felix Tshisekedi und Paul Kagame | Präsidenten DR Kongo und Ruanda
Hoto: SIMON WOHLFAHRT/AFP/Getty Images

Shugaba Joâo Lourenço na Angola ne ya yi ruwa ya yi tsaki na ganin bangarorin biyu da suka jima suna zargin juna sun hadu a Louanda, bayan sakewar rikici a tsakanin Kwango da makwabciyarta bisa zargin ba wa 'yan tawayen M23 tallafin makamai.

Sai dai ganawar mai cike da tasiri ga hukumomin ta bar baya da kura ga fararen hula, inda hare-haren 'yan bindiga suka sake kamari a wasu sassa na gabashin Kwangon. Da dama daga ciki sun gudu daga yankin Rutshuru don samun mafaka a waje, bayan da fada ya barke tsakanin dakarun Kwangon da mayakan M23.

Duk da haduwar Félix Tshisekedi da Paul Kagame da ke a matsayin ta tarihi don inganta hulda da kawo karshen zargin juna, ba a kawo karshen jin karar manyan makamai da ke tashi ba a wasu yankunan kasar Kwangon a daura da manufar taron na dinke baraka.

Sai dai shugaban wasu rukunin kungiyoyin fararen hula a yankin Rutshuru Jean-Claude Bambaze ya yi wa ganawar kakkausar suka duba da rashin tsinana komai da ta yi a zahiri ga rayuwar 'yan gudun hijira, yana mai bayyana haduwar a matsayin ta munafurci.

Rundunar tsaron Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na shan suka daga kungiyoyin fararen hula, inda suke bayyana cewa dole sai ta sake salon yaki da masu tayar da kayar bayan idan ana son samun zaman lafiya. Har yanzu batun tattauna tsakanin bangarorin da basa ga maciji bai samu gindin zaman ba a rikin da ya lakume dumbin al'umma a kasar Kwango.