1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin lardin Darfur na ci gaba da ruruwa

August 20, 2014

Rikicin da ya gudana tsakanin kabilun Sudan ya yi sanadiyar hallaka mutane 70 a Darfur da ke yammacin kasar Sudan.

https://p.dw.com/p/1CyPQ
Hoto: Getty Images

Wani tashin hankali da aka samu tsakanin wasu kabilun Larabawa biyu ya yi sanadiyar hallaka kimanin mutane 70 a Lardin Darfur na yammacin kasar Sudan mai fama da rikici.

Shaidun gani da ido sun ce an yi amfani da manyan makamai wajen lokacin rikicin tsakanin 'yan kabulan Rezeigat da kuma Maaliya. Irin wannan rikicin tsakanin kabilun biyu ya yi sanadiyar hallaka kusan mutane 200 a shekarar da ta gabata. Shekaru 11 ke nan aka washe na tashe-tashen hankula a cikin Lardin na Darfur da ke yammacin Sudan.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe