Rikicin makashi tsakanin Isra'ila da Masar
April 23, 2012Talla
Mr. Netanyahun ya bayyana hakan ne bayan da aka fara hasashen cewar dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta fara tsami, inda ya ce lamarin ya auku ne sakamakon wani saɓani na kasuwanci tsakanin ɓangarorin biyu.
A nata ɓangare, ƙasar ta Masar wadda ita ce ke samawa Isra'ilan kashi arba'in cikin ɗari na iskar gas ɗin da ta ke amfani da shi, ta ce lamarin ba haka ya ke ba, inda ta ƙara da cewar ta yi hakan ne saboda Isra'ila ta yi karen tsaye ga yarjejeniyar da su ka ƙulla game da cinikin isar Gas ɗin da ma dai tura shi ƙasar ta Isra'ila.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Abdullahi Tanko Bala