1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A matter of oil and death

January 17, 2012

Sudan da Sudan ta Kudu sun kiri taro a birnin Addis Ababa na kasar Etiopiya domin tattanawa game da takaddamar man fetur tsakanin su

https://p.dw.com/p/13kr9
(FILE) A file picture dated 19 January 2010 shows Sudanese President Omar el Bashir (R) and First Vice President and President of the Government of Southern Sudan, Salva Kiir Mayardit (L), participating in celebrations marking the 5th anniversary of the signing of the Comprehensive Peace Agreement (CPA) in Yambio, Sudan. Omar el Bashir has won the country's first multiparty elections in 24 years, election officials said on 26 April 2010. The polls are supposed to usher in a new era of democracy in Sudan, which is recovering from a decades-long civil war between the north and south. EPA/TIM MCKULKA - UNMIS - HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES +++(c) dpa - Bildfunk+++ Verwendung nur in Deutschland, usage Germany only
Omar el Bashir da Salva Kiir MayarditHoto: picture-alliance/dpa

A watan Juli na shekara da ta gabata yankin kudancin Sudan ya balle ya zama kasa mai cikkaken 'yanci, to saidai har yanzu tsugunne ba kare ba tsakanin Sudan da sabuwar kasar Sudan ta Kudu , mussamman game da albarkatun man fetur.

A wani mataki na warware takkadamar cikin ruwan sahi, tawagogin kasashen biyu sun fara zaman taro yau a birnin Addis Ababa na kasar Etiopiya.

Babbar matsalar dake ci gaba da rura wutar rikici tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu ta ta'allaka da mallakar albarkatun man fetur.

A halin da ake ciki yanzu, mafi yawan rijiyoyijn wannan arzikin karkashin kasa sun kasance a Sudan ta Kudu a yayin da hanyoyin da man ke kurara na cikin kasar Sudan.

Ra´ayoyin kasashen biyu sun bambanta game da kason man wanda su duka ke dogaro da shi domin samun kudaden shiga inji Wolf-Christian Paes shugaban cibiyar nazarin aiyuka a Kudancin Sudan dake nan birnin Bonn:

Karte Sudan nach Südsudans Unabhängigkeit!!! Ab 9.7.2011bitte nur diese Karte benutzen. ***Für mögliche Ergänzungen der Karte, wie z.B. andere Sprachen, zusätzliche Orte oder Markierungskreuz, wenden Sie sich bitte an infografik@dw-world.de (-2566), Außerhalb der Bürozeiten an bilder@dw-world.de (-2555).***

"Duk kasashen biyu takamarsu ta mai ce,a kudancin Sudan misali kashi 98 cikin dari na kudaden shiga su na zuwa ne daga cinakin man fetur, a Sudan kuwa, suna dogaro da mai daga kashi 70 zuwa 70 cikin dari na kudaden shigar."

Tun lokacin da Sudan ta Kudu ta balle, hukumomin Khartum suke ji a jikinsu illolin babban gibin da kasar ta samu ta fanin cinikayar man fetur.Alkalluman Asusun Ba da Lamuni na Duniya, sun tabatar da cewar kasar zata samu koma baya kashi 0,4 cikin dari na tattalin arziki.To saidai a daura da batun man fetur tawagogin kasashen biyu za su tattana game da wasu karin matsalolin dake hana ruwa gudu kamar yadda Kathelijne Schenkel daya daga jamai´an kungiyar Tarayya Turai dake aiki game da man fetur a Sudan:

"  tattanawar game da man fetur za ta tabo batun matsayin Abyei domin tantance bangaren da ya cencenci mallakar wannan yaki da kasashe biyu ke takkadama kansa,ta na yiwuwa sakamakon tattanawar a cimma matsayin bani gishiri in baka manda".

Akwai sabanin ra´ayin ainan tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu, domin gwamnatin Khartum ta bukaci sai hukumomin Juba sun biya Euro 28 kan ko wace gangar danyan mai da za a jigilar ta zuwa kasuwanin duniya ta hanyoyin bututun mai dake ratsawa a kasarsu, a yaiyn da Sudan ta Kudu tace za ta iya biyan centina 55 kacal.

Kungiyar kasashen Turai da ke bin diddikin al'amarin ta nuna damuwa kan yadda bisa dukan alamu taron ba zai iya cimma wani abun a zo a gani ba inji Wolf Christian Paes:

A Bari community member holds the flag of southern Sudan during celebrations on the eve of their declaration of independence in Juba, southern Sudan, Friday, July 8, 2011. Southern Sudan is set to declare independence from the north on Saturday. (Foto:David Azia/AP/dapd)
Tutar Sudan ta KuduHoto: dapd

" Makonin baya,Kasashen yammacin duniya sun bayyana matukar damuwa game da kiki-kakar da ake fuskanta tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu, to amma ba su da maganin matsalar.A hannu daya kasar China wadda ke da karfin fada aji a yankin,ba ta bukatar cenzawar al´amura."

Da dama daga masu nazarin al'amura a wannan yanki sun bayyana bukatar kasar China ta sa baki, domin kawo karshen takkadamar raban mai tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu, wadda da zaran ba a mangance ba, ba mamaki wani saban rikici ya sake barkewa a yankin baki daya.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu