Rikicin shugabanci a Ƙungiyar Taliban
August 3, 2015Iyalan tsohon jagoran Ƙungiyar Taliban Mollah Omar sun ki yin mubayi'a ga sabon shugaban kungiyar da aka zaɓa a makon da ya gabata tare kuma da yin kira ga shugabannin addini da su shiga tsakanin domin raba gardamar da ta dabaibaye jagorancin rikon kwarya na kungiyar. Iyalan Mollah Omar ɗin sun bayyana wannan matsayi nasu ne a cikin wani sako da suka wallafa mai dauke da muryar Mollah Abdul Manan kane ga marigayin.
A ranar Jumma'ar da ta gabata ne dai Ƙungiyar ta Taliban ta ba da sanarwar zaɓen Mollah Akhtar Mansur tsohon na hannun damar Mollah Omar ɗin a matsayin sabon shugaban Kungiyar 'yan tawayen ƙasar ta Afganistan. Matakin da dama tun kafin a je ko ina ya fuskanci adawa daga cikin 'ya'yan ƙungiyar da dama da ke zargin an gaggauta yin nadi sabon shugaban ba tare da an tsaya an samu fahimtar juna ba.