1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Siyasa a Senegal

April 2, 2007
https://p.dw.com/p/BuOP

Bayan ƙawacen da su ka girka, a sakamkon kayin da su ka sha, a zaɓen shugaban ƙasa, na ranar 25 ga watan Februaru,a Senegal, jam´iyun adawa bayyana aniyar ƙauracewa zaɓen yan Majalisun dokoki, da za a shirya watan juni mai zuwa.

Jam´iyun sun buƙaci a girka wata sabuwar hukumar zaɓe mai cikkaken yancin,saɓanin hukumar zaɓen yanzu, wadda a cewar su, yar amshin shata ce, ga gwmatin Abdullahi Wade.

Jam´iyun sun bayyana wannan sanarwa a yayin da ake shirye –shiryen rantsar da shugaba Abdullahi Wade bayan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa tun zagaye na farko.

Gobe idan Allah ya kai mu, aka shirya gudanar da wannan biki, tare da halartar shugabanin ƙasashe 14 daga sassa daban-daban na dunia, da kuma komishinan bada taimakon raya ƙasa na ƙungiyar gamayar turai Louis Michel.