Matsala kan yarjejeniyar raba iko a Sudan
July 26, 2019A wannan makon za mu fara sharhi da labaran jaridun Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda ta leka kasar Sudan tana mai cewa:
Duk da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin majalisar mulkin soji ta wucin gadi da wakilan kungiyoyi masu zanga-zanga a Sudan har yanzu ana fuskantar matsala wajen aiwatar da yarjejeniyar. Muhimmin batu da ake takkadama kai shi ne ko za a yi wa hafsoshin soji da ke da hannu a kisan gillan da aka yi wa masu zanga-zanga a ranar 3 ga watan Yuni, afuwa. Jaridar ta ce a ranar dakarun tsaro sun hallaka akalla mutane 120 a cikin masu zanga-zangar lumana a birnin Khartoum, sun yi wa mata kimanin 70 fyade. Jaridar ta ce a baiyane yake cewa dakarun ko-takwana na rundunar Rapid Support Forces suka aikata ta'asar duk da cewa shugabansu Mohammed Hamdan Daglo ya yi watsi da zargin. Jaridar ta ce ana cikin wannan kuma sai ga shi a tsakiyar wannan makon majalisar sojin wucin gadin Sudan din ta sanar da kame babban hafsan sojin kasar da wasu manyan hafsoshin soji kan wani sabon yunkurin juyin mulki da shi ne karo na biyar, tun bayan kifar da tsohon shugaban kasar Umar Al-Bashir. Wannan na nuni da cewa babu alamun samun masalaha nan kusa a rikicin na Sudan.
Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a wannan makon tsokaci kan mawuyacin halin da 'yan gudun hijirar Kamaru ke ciki a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya. Jaridar ta ce yakin da ake yi tsakanin gwamnatin Kamaru da 'yan tawayen yankin kasar da ke magana da harshen Ingilishi ya janyo wani mummunan yanayi na 'yan gudun hijira da bisa ga dukkan alamu ba ya daukar hankalin duniya. Tun a shekarar 2017 aka kafa sansanin Agadom da ke kusa da garin Ogoja na jihar Cross River a Kudu maso Gabashin Najeriya, inda gwamnatin Najeriya da hadin gwiwar Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisarn Dinkin Duniya suka tsugunar da 'yan Kamaru da suka tsere daga yankin masu magana da Ingilishi na Kamaru zuwa Najeriya. Yanzu haka dai an yi rajistar 'yan gudun hijirar Kamaru dubu 36 a sansanin. Jaridar ta ruwaito Hukumar Kula da 'yan gudun ta kasar Norway na cewa a halin yanzu babu rikicin 'yan gudun hijira da duniya ta manta da shi da ya kai na yankin Kamaru masu magana da Ingilishi.
Labarin yunkurin kisan wani matashi dan kasar Iritiriya a jihar Hesse da ke nan Jamus shi ya dauki hankalin jaridar Berliner Zeitung a wannan mako. Ta ce an yi wa wani matashi dan kasar Iritiriya mummunan rauni a wani lamari da masu bincike suka kwatanta da hari na kyamar baki. Jaridar ta ce bisa binciken da aka yi zuwa yanzu a fili yake cewa an harbi matashi dan shekaru 26 a ciki, saboda launin fatarsa. Bayanai sun kuma nuna cewa bayan binciken da aka yi a gidan mutumin da ya harbe shi, wanda daga bisani ya hallaka kanshi, sun tabbatar da wannan zargi. Yanzu haka an sallami matashin dan kasar Iritiriya daga asibiti. Jaridar ta kara da cewa ya zama wajibi a karfafa bincike don gano ko wanda ya aikata laifin mamba ne na wata kungiyar masu kyamar baki a Jamus.