1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Sudan da Sudan ta Kudu

April 19, 2012

Taƙaddamar da ke aukuwa tsakanin Sudan da Sudan Ta Kudu kan garin nan na Heglig mai arziƙin man fetur na ƙoƙarin jefa ƙasashen biyu cikin yaƙi.

https://p.dw.com/p/14hDd
Sudanese President Omar al-Bashir attends the opening of the second Arab-African summit in the coastal town of Sirte, Libya, 10 October 2010. According to media reports, the summit will hone in on key issues surrounding Palestinian-Israeli negotiations and the upcoming South Sudan referendum scheduled for January 2011, which could decide the future of a unified Sudan. This year's summit, organised by both the African Union and the Arab League, is the first for over 30 years. EPA/SABRI ELMEHEDWI +++(c) dpa - Bildfunk+++ usage Germany only, Verwendung nur in Deutschland
Omar al-BashirHoto: picture-alliance/dpa

Wannan kai ruwa ranar tsakanin ƙasashen biyu da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa ta sanya shugaban Sudan Omar Hassan al-Bashir cewar zai koyawa mahukuntan Sudan Ta Kudu hankali matsawar ba su janye dakarunsu daga Heglig ba wanda a cewarsa ya ke arewacin Kordofan saboda haka mallakin Sudan ne ba na Sudan Ta Kudu ba.

Shugaban Sudan Omar Hassan al-Bashir ya ce 'yan uwana lokaci ya yi da za mu fadawa juna gaskiya. Mun shirya mutuwa ko dai a Kahrtum ko kuma Juba. Jama'ar Sudan, musamman matasa mun daura ɗamarar yaƙi kuma da yaddar ubangiji za mu murƙushe waɗannan marasa gaskiya wato dakarun SPLA'.

To sai dai duk da waɗannan kalaman na shugaban Sudan, ita ƙasar Sudan Ta Kudun ta bayyana cewar ba ta shirin shiga yaƙi da Sudan ba kuma ba ta da niyyar haka kamar yadda ministan watsa labaran Sudan Ta Kudun Barnaba Marial Benjamin ya shaidawa manema labarai.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Zainab Mohammed Abubakar