Sudan: Sulhu da jagororin adawa
June 12, 2019Talla
Wani mai shiga tsakani na gwamnatin kasar Habasha ne ya tabbatar da hakan, sai dai kawo yanzu gwamnatin rikon da aka samar bayan hambarar da mulkin stohon shugabn mulkin kama karyar kasar Oumar al-Bashir ba ta kai ga tabbatar da labarin ba.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da wani babban jami'in gwamnatin Amirka ke shirin kai ziyara Sudan din, don shawo kan sojoji da su guji amfani da karfi kan masu zanga-zanga da ke son ganin lalle an kafa gwamnatin farar hula zalla.
Mutane fiye da 100 aka kashe a rikicin kasar ta Sudan, tun bayan da sojojin suka tarwatsa masu zanga-zangar adawa a ranar uku ga wannan wata na Yuni da muke ciki.