1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Sudan ta Kudu na fadada

January 17, 2014

Ana ci gaba da fafatawa tsakanin dakarun Sudan ta Kudu da 'yan tawaye cikin sassa daban-daban na kasar mai arzikin man fetur.

https://p.dw.com/p/1Asij
Hoto: Reuters

Ana ci gaba da fafatawa tsakanin dakarun gwamnatin Sudan ta Kudu da 'yan tawaye, inda yanzu haka ko wani bangare ke ikirarin yana iko da garin Malakal.

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi duk bangarori da hannu dumu-dumu wajen take hakkin dan Adam. An yi imani kimanin mutane 10,000 sun hallaka, tun lokacin da rikicin ya goce ranar 15 ga watan jiya na Disamba.

Kasar ta Sudan ta Kudu ta fada cikin sabon rikicin bayan Shugaba Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Riek Machar da yunkurin kifar da gwamnati. Yanzu haka sojojin kasar Uganda na cikin masu tallafa wa dakarun gwamnati.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman