1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Sudan ta Kudu ta ritsa da daruruwan rayuka

April 21, 2014

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa an hallaka mutane masu yawa da suka fake a wuraren ibada na sudan ta Kudu

https://p.dw.com/p/1BlgV
Hoto: AFP/Getty Images

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an hallaka daruruwan mutane cikin rikicin da yake ci gaba da ritsawa da kasar Sudan ta Kudu.

Rundinar dakarun kiyaye zaman lafiya na majalisar ta fitar da sanarwa wadda ke cewa an hallaka fiye da fararen hula 200, yayin da aka jikkata fiye da 400. Lamarin ya faru lokacin da 'yan tawaye masu dauke da makamai suka kame garin Bentiu a makon jiya, inda wani gidan rediyo ya bukaci mayaka su hallaka abokan gaba da suka fake a wuraren ibada.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu