1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Sudan ta Kudu ya rincaɓe

Usman ShehuDecember 19, 2013

Tashin hankali da ya ɓarke a Juba ya yaɗu zuwa wasu sassan ƙasar, inda 'yan tawaye suka karɓi iko da yankin samar da mai da ke da mahimmanci a tattalin arzikin ƙasar

https://p.dw.com/p/1Adi6
Shugaba Salva Kiir
Shugaba Salva KiirHoto: Reuters

Ƙasashen duniya sun fara kwashe 'yan ƙasashensu da ke ƙasar Sudan ta Kudu. Wannan kuwa ya biyo bayan rikincin da ya ɓarke bayan wani lamarin da gwamnatin ƙasar ta ƙira yunƙurin juyin mulki. A yanzu haka dai ofisoshin jakadanci na ci gaba da tattara 'yan asalin ƙasashensu da ke zama a ƙasar ta Sudan ta kudu, wanda ke zama ita ce jaririyar ƙasa a duniya.

Bayaga rikicin da ya ɓarke tsakanin sojojin da ke biyayya ga shugaban ƙasa Salva Kiir da kuma wadanda ke biyya ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa Riek Machar. Yanzu haka tashin hankali ya isa ga tsakanin fafaren hula. Inda wata gwabzawa da aka yi tsakanin ma'aikatan gwamnati abinda kuma ya yi sanadiyyar hallaka a ƙalla mutane 16. Ƙasashe kamar su Jamus, a yanzu haka sun tura jiragen soja biyu a yankin domin su kwaso Jamusawa da ma wasu 'yan ƙasashen waje da ke neman tserewa rikicin. DW ta tambayi Florian Dähne wakilin ƙidauniyar Friedrich Ebert a ƙasar a Khartum Sudan. Shin baya ga kwashe baƙin, ko akwai wani yunƙurin da ƙasashen duniya ke yi na sasanta rikicin?.

Südsudan Militär Soldaten ARCHIVBILD 2009
Sojoji cikin shiri a JubaHoto: Peter Martell/AFP/Getty Images

Yace, "Tabbas ina sane cewa ƙasashen duniya masu faɗa-aji na yin duk abinda za su iya don hana rikcin yaɗuwa. Suna tattaunawa da ɓangarorin biyu, inda suke nuna musu babu abin da zai kawo biyan buƙata illa tattaunawar kan teburi. Kana a nuna musu cewa matakin soji babu alfalun da zai haifar, illa ya ƙara jefa jaririyar ƙasar Sudan ta Kudu cikin wani bala'i, muddin ba'a shawo kan lamarin cikin gaggawa ba"

A halin da ake ciki dai wannan rikicin da ya ɓarke a Sudan ta Kudu, babu ɗayan biyu zai kawo cikas ga sake farfaɗo da ƙasar, inda yanzu haka ƙasashen duniya ke yunƙurin bata duk tallafin da za su iya domin ganin an sake ginata. Don haka bakin da ke gudanar da ayyukan raya ƙasa, dole su shiga fargaba kan rayuwansu. André Suren shi ne mai kula da ayyukan raya ƙasa a Sudan ta Kudu daga DW Akademie. Ya kuma bayyana irin damuwan da suka shiga kan ma'aikatansu da ke ƙasa yanzu haka Jonglei, yankin da a yanzu gwamnati ta tabbatar ya faɗa hannun 'yan tawaye.

Südsudan Riek Machar Vizepräsident Archiv 2011
Riek MacharHoto: Stan Honda/AFP/Getty Images

"A Jonglei mun samu yin magana da wasu muta ne, kuma lamarin da ke fitowa da ga yankin ya zarta yadda aka zata. Domin sojoji na gwabza faɗa mai ƙarfi. Faɗa sai ƙara zafi yake yi, kuma babu alaman zai lafa nan kusa. A yanzu lamarin ya tilastawa wasu mutane shiga cikin daji don tsira. Wannan ya jawo matuƙar buƙatar agajin gaggawa, domin a yanzu cikin rani ake a Sudan ta kudu, kuma wadanda suka tserewa faɗan na matuƙar buƙatar tallafi, musamman ruwan sha da abinci"

A cewar waɗanda suka son siyasar yankin Sudan ta Kudu dai, na cewa tuni suka hangi tashin hankalin zai ɓarke bisa alamun da ake gani a ƙasar. Inji Ulrich Delius, shugaban sashin Afirka na ƙungiyar kula da haƙƙin ƙananan ƙabilu masu fiskatar barazana.

Südsudan Juba Ausschreitungen UN Flüchtlinge 17.12.2013
Wadanda suka tsera wa tashin hanklinHoto: picture-alliance/AA

"Dama can muna gudun ɓarkewar rikicin ƙabilanci a Sudan ta Kudu. Tun gabanin yunƙurin juyin mulkin aka kai farmaki a kan ƙabilar Nuer. Akwai kuma wasu rahotanni da suka ce an kai hari kan ƙabilar Murle a Jonglei, don haka bisa wadannan misalen, tuni muka ga guguwar tashin hankali na kaduwa a Sudan ta Kudu".

Yanzu haka dai shugaban ƙasar Sudan ta kudu Salva Kiir, ya amince da ya gana da tsohon mataimakinsa Riek Machar, wanda ake ganin magoya bayansa ne suka yi yunƙurin kifar da gwamnati, abinda kuma a yanzu ke neman rikiɗewa izuwa wani mummunan rikicin ƙabilanci.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani