Jaridun Jamus kan hambarar da al-Bashir
April 12, 2019A sharhin da ta rubuta jaridar Der Tegeszeitung ta fara ne da cewa al'umar kasar Sudan sun cancanci yabo dangane da faduwar daya daga cikin shugabannin mulkin kama karya na wannan zamani. Jaridar ta ce shekaru 30 da suka gabata al-Bashir tare da taimakon sojoji da kuma kasar Iran ya karbi mulki a Sudan, inda ya tafiyar da mulki na kama karya ciki har da ta'asar da aka aikata a yankin Darfur, da yakin basasa da yankin kudancin kasar. A dangane da zargin aikata kisan kare dangi, kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ta ba da sammacin kama shugaban mai shekaru 75. Yanzu mulkinshi ya kawo karshe godiya ta tabbata da boren da 'yan kasar suka shafe watanni suna yi na ganin ya sauka daga karagar mulki. Jaridar ta karkare sharhin da jinjina wa matan kasar musamman ma Alaa Salah 'yar shekaru 22 wadda jaridar ta bayyana da zama alamar juyin juya halin bisa dagewar da ta yi tana tsima masu zanga-zangar da ka da su yi kasa a gwiwa.
Sojojin Sudan sun yi waje road da al-Bashir wannan shi ne taken labarin da jaridar Neues Deutschland ta buga game da halin da ake ciki a Sudan, amma bisa ga dukkan majalisar mulkin rikon kwarya da sojojin suka kafa ba ta kai ga gamsar da masu zanga-zanga da suka lashi takobin ci gaba da tayar da kayar baya har sai an kafa gwambatin mulkin farar hula. A jawabin da jagoran majalisar mulkin sojin Awad Ibn Auf ya yi, ya ce sojojin za su kwashe shekaru biyu a kan karagar mulki, sannan ya kafa dokar ta-baci don hana ci gaba da zanga-zanga. Sai dai masu boren sun ci gaba da nuna rashin amincewarsu da sabuwar majalisar mulkin sojin suna zargin cewa babu maraba tsakanin shugaban rikon kwarya da tsohon Shugaba al-Bashir, kasancewa shi ne ministan tsaron kasar karkashin al-ashir yana kuma da hannu a yawancin aika-aikatar da gwamnatin kasar ta tabka.
Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung a wannan makon ta sake lekawa kasar Ruwanda inda a karshen makon da ya gabata aka fara bukukuwan cika shekaru 25 da kisan kare dangin da ya faru a Ruwanda a 1994. Jaridar ta ruwaito Shugaba Paul kagame na Ruwandan ya na cewa kisan kare dangi ya dakushe duk wani fata, amma talakawan kasar sun jajirce sun tsaya tsayin daka sun taimaka wa kasarsu ta sake farfadowa. Daga cikin manyan bakin da suka hallara a birnin Kigali a ranar Lahadi akwai Shugaban hukumar kungiyar tarayyar Turai Jean-Clude Juncker da ya ce bikin nuna alhinin ga wadanda ta'asar ta rutsa da su ya sosa masa zuciya. Tsohon shugaban Jamus Horst Köhler ya wakilci kasarsa. Mutane kimanin dubu 800 daukacinsu 'yan Kabilar Tutsi da masu sassaucin ra'yi na Hutu aka yi kiyasin 'yan Hutu masu matsanancin ra'ayi sun yi wa kisan kare dangi.