1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Rikicin Hausawa da yan kabilar Berti

July 20, 2022

Ministan kiwon lafiyar kasar Jamal Nasser ya ce duk da jami'an tsaro sun taimaka wurin dakile rikicin kabilancin, kawo yanzu mutane 291 lamarin ya raunata.

https://p.dw.com/p/4EQdl
Sudan Hausa Protest in El-Obeid
Hoto: AFP


Mutanen da rikicin Hausawa da kabilar Berti ya halaka a Sudan sun kai 105. A ranar Asabar da ta gabata aka fara rikicin a yankin Sudan da ke makwabtaka da kasashen Habasha da Sudan ta Kudu. Lokaci zuwa lokaci dai rikicin kabilanci kan mallakar filaye irin wannan kan faru a kasar ta Sudan da ke a gabashin Afirka.