1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Rikicin yankin Darfur na Sudan ya ci rayuka

December 17, 2021

Kwararru a Sudan, sun ce dole ne gwamnatin kasar Sudan ta kawo karshen asarar rayuka da ake yi a yankin Darfur. Sama da mutum dubu 80 ne suka rasa muhalli a yankin.

https://p.dw.com/p/44Ur3
Sudan West Darfur | Rauchwolken im Abu Zar Camp
Hoto: AP/picture alliance

Likitoci a Sudan, sun ce kimanin mutum 200 ne aka kashe a yankin Darfur na kasar sakamakon rigingimun kabilanci da suka faru cikin watanni biyun da suka gabata.

Kungiyar likitocin wadanda ba na gwamnati ba, su ne suka tabbatar da cewa akwai mutum 199 da suka salwanta a rigingimun, kuma galibin su an kashe su ne da tsinin bindiga.

Likitocin wadanda ke jan hankalin gwamnati da ta dauki matakan dakatar da zubar jini a yankin na Darfur, sun nuna takaicin rashin kwarararn matakan hana kashe-kashen daga mahukuntan na Sudan.

A cewar kungiyar da ke kula da kaurar jama'a ta duniya IOM, akwai sama da mutum dubu 83 da rigingimun suka raba da muhalli.

Tun cikin shekara ta 2003 ne dai yankin na Darfur a Sudan ya fada rikici musamman na tawaye da tsirarun kabilu suka kafa.