Rincabewar rikicin Sudan ta Kudu
December 20, 2013Majalisar Duniya Duniya ta fadi - a wannan Jumma'ar cewar, akalla fararen hula 20 dake samun mafaka a wani sansaninta dake kasar Sudan ta Kudu ne, wasu mahara suka yi wa yankan rago, inda kuma wasu Indiyawa biyu da ke yin aikin wanzar da zaman lafiya ma suka mutu. Wata sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ta ce kimanin matasa 'yan kabilar Nuer dubu biyu ne suka afkawa sansaninta dake Akobo na jihar Jonglei, inda fararen hula 'yan kabilar Dimka 36 ke samun mafaka, kana akalla 20 daga cikinsu suka mutu sanadiyyar farmakin. Sai dai a yanzu wasu ministocin harkokin wajen Kungiyar Kasashen Gabashin Afirka sun isa birnin Juba, inda suka gana da shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu gabannin ganawa da masu adawa dashi, a kokarin shiga tsakanin da Kungiyar Tarayyar Afirka ke yi domin kawo karshen rikicin baya bayannan da ya barke a kasar.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu