Rousseff ta lashe zaɓe a Brazil
November 1, 2010Dilma Rousseff ta zama mace shugabar ƙasar Brazil ta farko bayan ta lashe zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu da aka shirya jiya Lahadi a faɗin ƙasar baki ɗaya.
Rousseff mai shekaru 62 a duniya ba ta taɓa shiga takarar zaɓe a baya ba, sai dai ta kasance majidaɗin shugaban ƙasa mai barin gado, Luiz Inacio Lula da Silva wanda ya samu farin jini a ƙasar ta Brazil. Ta lashe zaɓen da kashi 56 cikin 100 na yawan ƙuri'un da aka kaɗa, a yayin da abokin hamayarta Jose Sera ya samu kashi 44 cikin 100.
Sabuwar shugabar ƙasar ta yi alƙawarin koyi da shugaba Lula da Silva ta fannin yaƙi da talauci da haɓaka tattalin arzikin ƙasa.
"Zan yi aiki bil haƙƙi da gaskiya ba tare da nuna wariya ba ga dukkanin al'umar ƙasar ba. A yanzu na zama shugabar duk al'umar Brazil gaba ɗaya."
Za a rantsar da Dilma Rousself a ranar ɗaya ga watan Janeru na shekara ta 2011.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal