1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rubu'in miliyan 'yan Rohingya na neman mafaka

Yusuf Bala Nayaya
September 8, 2017

Wannan adadi na zama abin tada hankali a cewar Vivian Tan mai magana da yawun sashin kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/2jahv
Rohingya fliehen nach Bangladesch
Hoto: picture-alliance/dpa/N. Islam

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a ranar Juma'an nan cewa Musulmi 'yan kabilar Rohingya 270,000 ne suka kauracewa tashin hankali a Myanmar inda suka nemi mafaka a Bangaladash cikin makonni biyu.

Wannan sabon adadi na zama abin tada hankali a cewar Vivian Tan mai magana da yawun sashin kula da 'yan gudun hijira na MDD, wacce tace adadin ya zarce wanda MDD ta bayyana da cewa sun shiga Bangaladash tun daga ranar 25 ga watan Agusta.

Ta ce adadin ya zarce yawan sansanoni da aka tanada da kayan agaji wannan kuwa duk da tallafin da al'umma a wasu yankuna na kauyika a Bangaladash ke bayarwa wuraren kuma da ke zama da wahala akai agaji wajen.