1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudani a majalisar dokokin Najeriya

Uwais Abubakar IdrisJune 25, 2015

Kwadayin shugabanci ya sa fada ta kaure tsakanin 'yan majalisar Tarayya. Hayaniyar dai ta barke ne bisa zaben shugabanin jamiyyar APC mai mulki inda kuma hakan ya sa aikin majalisar ya tsaya cik.

https://p.dw.com/p/1FnMU
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

An dai samu bambancin ra’ayi ne a tsakanin masu son ganin an bi umurnin jamiyyar ta APC bisa mutanen da take so a zaba, da wadanda ke son majalisar ta yi radin kanta a kan wannan batu.

A fili take cewa tsugune bata kare ba a majalisar dattawan Najeriyar, domin kuwa duk da kokari na sa baki da gwamnonin jamiyyar APC da ma uwar jamiyyar ta yi a kan batun shugabancin majalisar, bangarori biyu na shugaban majalisar Sanata Bukola Saraki da Sanata Ahmed Lawan, wanda yake ganin an mashi yankan baya a zaben majalisar na ci gaba da nunawa juna ‘yar yatsa. Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fassarari rikicin majalisar da cewa.

Rabiu Musa Kwankwaso
Hoto: DW/T. Mösch

‘’Ai magana ce ta a wurin talakan Najeriya ka zabi, da wannan da wancan wanne ka ke so. Ga wasu ma jamiyyun, domin ba tsarin daya bane, idan da a jamiyyar APC da PDP duk daya ne ai da duk mu da ‘yan PDP sai mu shiga majalisar mu zauna. Kuma yau shekarar PDP 16 tana tafiyar da al’mmuranta a majalisar nan bata taba shigar da wani cewa ya zo ya shigo ba, amma saboda sakaci namu da son zuciya da wasu cikinmu, na sai sun bata abinda ba nasu ba, to in bamu nan aka yi to ba wanda zai aske mana gashin kanmu bama wurin’’.

Kashedin da jamiyyar ta APC ta yi wa yayanta na su zabi Sanata Ahmed Lawan din a matsayin shugaban masu rinjaye ya bi ta bayan kunnen wasu ‘yan majalisar da ke bayan Sanata Bukola Saraki,. To sai dai sakataren jamiyyar ta APC Mai Mala Boni, yace ya zama dole su tabbatar da cewa abinda jamiyyar ta tsara shi ne zai faru.

Nigeria Oppositionspartei APC
Hoto: DW/K. Gänsler

‘’Jamiyyar APC tana da hurumi a kan abinda ya kamata ya faru a majalisa, a kan wadanda take ganin sune za su yi mata jagoranci a majalisa. Kuma abinda muka yi shi ne mun yi sulhu ne na yadda jamiyya za ta tafi a dunkule na dukkanin yayan jamiyyar a majalisar, wanda kuma mu a tsamanimu ba wanda zai fito a jamiyyar ya yi mana terere’’.

A yayinda ake tirka-tirka a majaloisar wakilan Najeriyar majalisar datawan ta amince da sunayen da aka mika mata na Sanata Ali Ndume a matsayin shugaban masu rinjaye, yayinda Sanata Bala Na’Allah a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye abinda ya nuna watsi da matsayin jamiyar. Ko wane kalubale suke hasashen fukanta? Har ila yau ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

‘’Ai ba za’a sasauta ba, saboda akwai ‘yan sa kafar ungulu a gefe ko a tsakiya, wannan na tabbata cewa shugabanin jamiyyarmu za su tabbatar an samu nasara. Mu ma muna nan a bangaren majalisar zamu ga duk abimnda zamu yi domin tabbatr da cewa wadanda ke son su kawo mana cikas basu samu nasara ba’’

Abin jira a ganin shine yadda za ta kaya a majalisar a dai dai wannan lokaci da nasarar da jamiyyar APC ta samu ke zama samun dan tsako an rasa zama a ci moriyarta.