1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin ceto mutane daga baraguzan ginin da ya rushe

Ramatu Garba Baba AH/MAB
November 2, 2021

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas a Najeriya, ta ce mutum 6 ne aka tabbatar suka mutu daga cikin mutune sama da dari da ake fargabar dogon bene ya rufta a kansu.

https://p.dw.com/p/42RdU
Nigeria Gebäudeeinsturz in Lagos
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Wani babban jami'in hukumar bayar da agajin gaggawa, Olufemi Oke-Osanyintolu, ya ce ma'aikatan agaji na ci gaba da aiki tukuru don ganin an zakulo sauran mutanen da ke karkashin ginin.

Benen mai hawa ashirin da biyar da ke unguwar Ikoyi, daya daga cikin ungwanin masu hannu da shuni, ya rufta kan masu aikin ginin benen ciki har da wanda ke aikin kwangilan ginin.

Al'ummar jihar Legas cibiyar kasuwancin Najeriya ta tsinci kai cikin rudani bayan wannan ibtila'in da ke faruwa bayan wani wanda ya auku a shekarar 2019, inda wani dogon benen ya fada kan wata makaranta tare da kashe dalibai kimanin 20.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun rushewar bene ko gini ba a jahar Legas. Hukumomi a Najeriyar na danganta yawaitar rushewar gine-gine da rashin bin tsarin gini da ma rashin ingancin aiki.

A shekarar 2019 wani dogon bene ya fada a kan wata makaranta tare da kashe dalibai 20 kusan 40 sun jikkata.