SiyasaAfirka
Sudan: Ruftawar mahakar zinare ta kashe mutane sama da 30
December 28, 2021Talla
Kimanin mutane 31 ne suka mutu a yayin da wata mahakar zinare ta rufta a kasar Sudan. Ma'aikatar kula da albarkatun kasa ta sanar a dazu da rana cewa akwai karin wasu mutane takwas da suka samu munanan raunuka. Lamarin dai ya faru ne a garin Al-Nuhud da ke yamma da yankin Kordofan.
Zinare dai na daga cikin hanyoyin da kasar ta Sudan da ke a gabashin Afirka ke samun kudin shiga. Sai dai galibin wuraren da ake hakar zinaren na aiki ba tare da sahalewar hukumomi ba.