Rundunar MDD ta gama aiki a kasar Haiti
October 6, 2017Talla
Shugabar rundunar ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Haiti Sandra Honore ta ce har yanzu akwai sauran ayyuka da dama da ta kamata a yi a kasar ta Haiti kafin ta kai matsayin da kowane dan kasar ke fatan gani.
A shekara ta 2004 ne dai aka girka rundunar ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Haiti bayan ficewar shugaban kasar Jean-Bertrand Aristide domin kwantar da tashe-tashen hankulan da aka fuskanta musamman a Port-au-Prince babban birnin kasar, sai dai kuma rundunar ba ta samu yarda daga 'yan kasar ba, musamman magoya bayan tsohon shugaban kasar.