Sa In Sar Falasdinu da Isra'ila
July 25, 2017Talla
Batun tsaurara tsaro da na'urori a masallacin da musulmi ke darajawa a makon jiya dai, ya haddasa fito-na fito tsakanin musulmi da kuma Isra'ilawa. Su dai falasdinawan sun kekashe kasa ne, suna mai cewa sun kure hakurinsu bayan kwace masu yankuna, yanzu kuma Isra'ilar ta hau kan masallacin na Al Aqsa da suke karramawa.
Wannan dai waje ne da ke da muhimmanci ga musulmi da yahudawa gami da mabiya addinin kirista. A wannan Litinin, gwamnatin Isra'ila ta soma janye na'urorin binciken da ta kakkafa a kofofin shiga masallacin. Kuma bayan matsin lamba daga bangarori daban-daban na duniya, jami'an tsaron Isra'ilar sun fada a yau Talata cewar za su amince da shawarwarin cire matakan tsaron da suka sanyawa wajen.