1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Siriya: Karuwar hare-haren ta'addanci

Kersten Knipp LM
December 4, 2024

Mayakan da ke ikirarinin jihadi sun koma kai hare-harei a kan gwamnatin Bashar al-Assad. Sai dai kuma za a iya cewa kawo yanzu, hare-haren nasu bai yi wata mummunar illah ga gwamnatin kama-karyar ta Siriya ba.

https://p.dw.com/p/4nkT2
Siriya I Shugaban Kasa | Bashar al-Assad | Mayaka | Jihadi | Hare-hare
Tsugune ba ta kare ba, ga shugaban Siriya BAsha al-AssadHoto: SANA/Photoshot/picture alliance

Duk da wannan sababbin hare-hare da mayakan masu ikirarin jihadi suka koma kai wa a Siriya, Shugaban Bashar al-Assad da kujerar mulkinsa ta tsira da kyar a yakin basasar kasar ka iya asamun agaji. 'Yan fafutuka sun sanar da shigar mayakan Shi'a daga Iraki daga gabashin kasar ta Siriya, inda suke yaki kafada da kafada da mayakan gwamnati da ke yakar 'yan tawaye. 'Yan tawayen dai sun koma kai hare-harensu ne a makon da ya gabata, inda suka fara da birnin Aleppo. Sun fatattaki sojojin gwamnati daga birnin, tare da kame shi. Rahotanni sun nunar da cewa kimanin mayaka 200 da ke goyon bayan Iran ne suka tsallaka kan iyakar Siriyan daga Iraki, kuma gwamnatin Assad ka iya dora tsammanin samun agaji daga Rasha ma. Kamfanin dillancin labaran Rashan ya ruwaito kakakin fadar gwamnatin Kremlin Dmitry Peskov na cewa: "tabbas za mu ci gaba da marawa Bashar al-Assad baya." Tuni ma dai sojojin Rashan da hadin gwiwar na Siriyan suka kaddamar da hare-hare a karshen mako, a kan mayakan Haiat Tahrir al-Sham (HTS) da ke ikirarin jihadi a Siriyan.

Siriya | Aleppo | Mayaka | Jihadi | Hare-hare
Siriya ta fuskanci sababbin hare-hare daga masu ikirarin jihadi Hoto: Juma Mohammad/AP Photo/picture alliance

Kungiyar ta mayakan HTS da ke da alaka da wadanda ake kira wai da Syrian National Army (SNA), wato hadakar 'yan adawar Siriya da ke da alaka da Turkiyya. Masu fashin baki kamar kwararre kan Siriya a Cibiyar Nazarin Al'amuran Duniya da Yankuna ta Jamus GIGA André Bank na da ra'ayin cewa, yadda HTS ta yi nasarar yin wannan gagarumin kutse ba tare da ta samu cikas ba, ka iya zama yana da alaka da lokacin a ta zabi ta kai harin. Bank ya kuma shaidawa DW cewa, ana iya yin la'akari da yadda Iran da Hezbollah suka mayar da hankulansu kan yaki da Isra'ila kana Rasha na fama da yaki da makwabciyarta Ukraine. A cewarsa HTS ta mayar da hankali wajen gina kanta, inda ta zama kungiyar masu ikirarin jihadi mafi karfi a yammacin Siriya. Bank ya ce burin HTS ba wai ta yi jihadi a duniya ba ne ta mayar da hankalinta ne kwacokam kan Siriya, inda ta ayyana kanta a matsayin jirgin ceto kasar.  A yanzu kungiyar na amfani da mayan makamai masu linzami da kuma jiragen yaki marasa matuki, wanda za a iya zargin cewa sun shigo hannunsu ne ta hanyar Turkiyya.