Sabbin matsugunan Yahudawa a yankunan Falasɗinawa
December 1, 2012Isra'ila ta sanar da shirin gina sabbin gidaje dubu ukku a yankunan Falasɗinawa da take ci gaba da mamayewa a gaɓar kogin Jordan da kuma gabashin birnin Qudus. Wannan sanarwar ta zo ne yini ɗaya kachal bayan da babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya baiwa Falasdinu kujerar 'yar kallo a cikin zauren. Daga cikin wuraren da Isra'ila za ta yi gine-ginen dai harda yankin nan da ake yiwa lakaɓi da E1, wanda ya rarrabe tsakanin arewaci da kuma kudancin yammacin kogin Jordan. Idan har ta aiwatar da wannan kudirin dai, hakan zai rarrabe tsakanin yammacin kogin Jordan din kenan, wanda zai sa Falasdinawa su fuskanci matukar wahala wajen yin zirga-zirga daga arewaci zuwa kudancin yankin. Amirka dai ta yi suka ga Isra'ila bisa bayyana wannan shirin, tare da ambata hakan a matsayin wanda ba zai haifar da sakamako mai kyau ba a kokarin samar da zaman lafiya a yankin.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou