Sabbin takunkumi ga Rasha
February 9, 2021Talla
Josep Borrell ya ce ya zama wajibi kasashen 27 na kungiyar su sami kwakwarar matsaya ciki har da amfani da sabbin takunkumi dangane da daurin talala da ta yi wa jagoran adawar kasar Alexei Navalny.
Borrell ya ce zai gabatar da tayin daukar matakin idan ya jagorancin taron kungiyar na ministocin harkokin ketare a ranar 22 ga watan Fabarairun nan.
An dai kama jagoran adawa kuma mai caccakar gwamnatin Shugaba Putin a watan Janairu bayan ya dawo daga jinyar da ya yi a Jamus sanadiyar gubar da aka sanya masa. Tuni dai kungiyar EU ta sanya takunkumi ga wadanda ke da hannu a sanya masa gubar sai dai Navalny ya bukaci a sanya musu takunkumi tafiye -tafiye da toshe asusun ajiyar manya 'yan siyasa da ke zama na hannun daman shugaba Putin.