Sabbin 'yan tawaye a Sudan ta Kudu
June 28, 2016Wani babban jami'in gwamnatin sudan ta Kudu ya yi zargi an kafa wata kungiyar 'yan tawaye domin kifar da gwamnatin kasar, watanni bayan fara aikin da yarjejeniyar gwamnatin hadaka.
Michael Makuei Lueth ministan yada labarai ya shaida wa manema labarai a wannan Talata cewa wani dan siyasa mai suna Ali Tamin Farkak ya kaddamar da tawaye cikin lardin Wau, inda aka yi dauki ba dadi da sojojin gwamnati abin da ya janyo mutuwar kusan fararen mutane 40, da 'yan sanda hudu. A cewar ministan na Sudan ta Kudu 'yan tawayen suna samun goyon baya daga 'yan tawayen LRA na Yuganda.
Tuni gwamnatin Sudan ta Kudu ta bayyana rashin gudanar da shagulgula yayin da ake bikin samun 'yanci daga Sudan a ranar 9 ga watan gobe na Yuli saboda matsalolin da sabuwar kasar ta Sudan ta Kudu ta samu kanta a ciki.