Sabin dubarun yaƙi da yaɗuwar cutar Ebola.
October 16, 2014Talla
Wannan labari ya fito ne a wannan Alhamis din(16.10.2014) daga hukumar lafiya ta duniya WHO wadda kuma ta ce ba ta ba da shawarar cewa da a tsaurara matakan bincike ga filayan jiragen sama ba. Ƙasashen da ke kan gaba wajan samun wannan tallafi dai sun hada da Cote d'Ivoir, Gini Bissau, Mali da Senegal. Sai kuma wasu Ƙasashe 11 da suka hada da Ƙasar Benin da Burkina Fasso da Kamarun, Gambiya da Ghana da Mauritaniya, da Najeriya da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Kwango da Sudan ta Kudu da kuma Togo. An zaɓi waɗannan ƙasashe ne dangane da hanyoyin su na kasuwanci da kuma tsarin kiwon lafiyar su a cewar Isabelle Nutall jami'ar kula da rigakafi a hukumar ta WHO a Geneva.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahmane Hassane