1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kawo karshen zaman doya da manja a Sudan ta Kudu

Lateefa Mustapha Ja'afarAugust 25, 2015

Masu shiga tsakanin a rikicin Sudan ta Kudu sun sanar da cewa shugaban kasar Salva Kiir ya yi alkawarin sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu.

https://p.dw.com/p/1GLTn
Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu
Shugaba Salva Kiir na Sudan ta KuduHoto: picture-alliance/dpa/P. Dhil

Al'ummomin kasa da kasa dai sun dade suna kira ga bangarorin da ke gaba da juna a Sudan ta Kudun da su kawo karshen rikicin kabilancin da kasar ta tsinci kanta a ciki na tsahon watanni 20. Kungiyar ci-gaban kasashen yankin Gabashin Afirka IGAD da ke shiga tsakani ce ta sanar da batun sanya hannu, inda ta ce Kiir ya ce zai rattaba hannun a kan yarjejeniyar sulhun a wannan Larabar 26 ga watan Agusta da muke ciki a birnin Juba na Sudan ta Kudun. Matakin nasa dai na zuwa ne kwanaki biyar bayan da Amirka ta kudiri aniyar tabbatar da ganin an sanya wa kasar takunkumin karya tattalin arziki sakamakon rikicin da yaki ci yaki cinyewa. Tun dai a ranar 18 ga wannan wata na Agusta da muke ciki ne abokin hamayyarsa kuma tsohon mataimakinsa Riek Machar ya sanya hannu kan yarjejeniyar sulhun domin kawo karshen rikicin kabilancin da ya jefa al'ummar kasar cikin halin tasku.