1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon harin ta'addanci a Mali

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 6, 2017

Wani harin ta'addanci da aka kai a shalkwatar sojojin kasar Mali da ke kusa da kan iyakar kasar da Burkina Faso, ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin kasar Malin 11 tare kuma da jikkata wasu guda biyar.

https://p.dw.com/p/2YgaB
Mali na ci gaba da fuskantar hare-haren ta'addanci
Mali na ci gaba da fuskantar hare-haren ta'addanciHoto: picture-alliance/Photoshot

Kakakin ma'aikatar harkokin kasashen ketaren Malin wanda ya tabbatar da afkuwar harin ya nunar da cewa tuni aka kara yawan jami'an tsaro a wajen, sai dai bai yi karin haske kan ko an kama maharan ba ko kuma sun tsere. Kawo yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta dauki nauyin kai wannan harin, sai dai a watannin baya-bayan nan masu kaifin kishin addini da suka hadar da kungiyoyin da ke da alaka da al-Qaeda sun kai hare-hare kan sojojin kasar ta Mali, kana kungiyar 'yan ta'addan Ansar ma ta kai hare-hare masu yawa a kan jami'an Majalisar Dinkin Duniya da sauran yankuna a kasar, a kokarin da take na yada abin da ta kira da Jihadi a yankunan da masu sanya idanu na kasa da kasa suka bayyana da cewa basu da hadari a kasar.