Sabon rikici ya sake barkewa a kasar Sudan
June 12, 2023Talla
Tun a jranar lahadi ne aka fara jin karar fashe-fashe a birnin Khartoum, wanda mazauna garin suka ce shi ne irin shi mafi muni a baya-bayan nan.A Ondurman ma, rahotannin sun tabbatar da ci gaba da ruwan makamai irin na atilare. A baya, an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin da ke gaba da juna, sai dai ba ta yi wani tasiri ba.
Amirka da Saudiyya da suka taimaka aka cimma yarjejeniyar a baya sun ce wannan tsagaita wuta an sami damar kai wa mabukata daukin gagawa. Rikicin da ya samo asali a kan neman shugabanci na ci gaba da lakume rayukan mutane tatre ma da raba dubbai da matsugunnansu.