Sabon rikicin kabilanci a Sudan ya halaka mutane
July 27, 2020Talla
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da harkokin jinkai a kasar Sudan ya ce a ranar Asabar rikicin ya kaure a tsakanin kabilar Masalit da wasu Larabawa a kauyen Masteri da ke lardin Darfur na yammacin kasar Sudan.
Rahotanni sun ce rikicin ya ci gaba da gudana har zuwa safiyar Lahadin da ta gabata, inda kafin kura ta lafa, sai da aka raunata mutane da yi wa jama'a sata da kuma bankawa kasuwar kauyen wuta. Tuni dai hukumomi suka jibge sojoji a yankin don dakile harin ramuwar-gayya.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin kabilancin na zama wata babbar barazana ga zaman lumanar kasar ta Sudan tun bayan tsige tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir a shekarar da ta gabata.