Sabon shirin tsaron tekun Bahrum
September 14, 2016Talla
Rundunar za a bata ikon kula da jiragen ruwa da ke bin tekun na Bahrum kuma suna da ikon bincikan duk wani jirgin ko kwale-kwale da su ke tuhuma yana dauke da mayakan kungiyoyin tarzuma kamar na IS. A cewar rahoton da A cewar mujallar Der Spiegel, ta wallafa, wani karin aikin da rundunar mai suna Operation Sea Guardian za ta yi, zai hada da takaita masu fataucin mutane da wadanda ke yin simogan makamai, a yayinda rundunar ke lura da kan iyakokin kungiyar Tarayyar Turai. Ana fatan kasar Jamus za ta bayar da kimanin sojoji 650, da za su yi aiki cikin rundunar.