Shugaban Najeriya ya fara sabon wa'adi cike da kalubale
May 29, 2019
Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin sa Ferfesa Yemi Osinbajo sun yi rantsuwa a dandalin Eagle square a birnin tarayya Abuja a gaban daruruwan mutane ciki harda jami’an diplomasiya na kasashen ketare da kuma jagororin jamiyyar APC mai mulki a Najeriya da tsoffin ministoci da makaraban gwamnati gami da magoya bayan shugaban.
Wannnan dai shi ne karo na biyu da Shugaba Muhammadu Buhari ya sake dawowa madafun iko a Najeriya kasar kuma da ke cike da tarin kalubale kama daga na tsaro, tattalin arziki, rashin aikin yi a tsakanin milyoyin matasa gami da matsalar baya-bayan nan ta yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa na daga cikin batutuwan da shugaban zai tinkara a shekaru hudu da ke tafe.
Mafi yawancin ‘yan Najeriya dai na kallon shugaban a matsayin mai halin dattaku da nuna gaskiya gami da kishin kasarsa kuma mutum ne mara tsoro wajen yaki da cin hanci da karbar rashawa a inda a gefe guda wasu ke kallon gazawar gwamnati wajen daukar matakan da suka dace domin dora kasar a turba ga batun alkawuran da gwamnatin ta dauka a baya.
‘Yan Najeriya sun zuba idanu domin kallon zubin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari wa’adi na biyu musamman a bangarorin tsaro da yaki da cin hanci da kuma gyara tattalin arzikin kasar da talawa za su amfana.