1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Chaina da Amirka na barazana ga duniya

Usman Shehu Usman GAT
May 29, 2020

Takun sakar da ake yi tsakanin kasashen Chaina da Amirka ta hanyar shugabanninsu na taimakawa ga rura watar rigingimun da ke addabar duniya a wannan zamani.

https://p.dw.com/p/3czxt
Donald Trump
Hoto: Reuters/J. Ernst

Za a dai iya cewa tun bayan kawo karshen yakin duniya na biyu, ba wani lokacin da duniya ta shiga cikin hatsarin da rikicin siyasa kamar wadannan shekaru da Donald Trump ya shugabanci Amirka. Yayin da matakan Trump kan Iran suka yi kusan jefa duniya cikin yaki, yanzu kuma Trump da Chaina sun bude wani sabon babi na kalaman batanci tsakaninsu. 

A karon farko dai an jiyo ministan harkokin wajen Chaina na ambatar kalmar yakin cacar baka. Wanda kalma ce ba a cika jinta daga bakin shugabanni ba, musamman kasar Chaina da ke zama 'yar ba ruwanmu a baya. Ministan ya yi kalaman ne yayin jawabi gaban majalisar al'ummar kasar Chaina wacce ta amince da dokar bai wa Chaina karin ikon sa baki a rikicin Hong-Kong in ji Josef Braml kwararre a cibiyar siyasa da tattalin arzikin Jamus:
  
"A nawa ganin wasu na cewa wannan annobar corona ta kawo sauyin tsarin walwala na duniya wajen abokantakar kasashen duniya. Amma ba haka ba ne. abin da ke faruwa shi ne kara lalata huldar Amirka da hadin kai na tattalin arziki kana ya kawo barkewar takaddamar tsakanin Amirka da China"

China Präsident Xi Jinping
Hoto: picture-alliance/dpa/X. Huanchi

Tun gabanin barkewar annobar Coronavirus ne dai, shugaban Amirka Donalad Trump ya tsauwala haraji bisa kayakin da Chaina ke shigarwa kasar abin da ya fara jawo rikici tsakanin mayan kasashen biyu da suka fi karfin arzikin masanana'antu a duniya. Bugu da kari Shugaba Trump ya sa idanunsa bisa kamfanin sarrafa wayoyi mallakar kasar Chaina wato Wuawei, inda yake neman kasashen Turai kamarsu Jamus da Birtaniya da kar su yi hulda da kamfanin na Chaina a cewar Sebastian Heilmann, masani kan siyasar kasar Chaina: 

"Kamfanin Huawei ba wai a matsayin kamfani kawai yake ga Chaina ba, amma ya kasance a matsayin babbar cibiyar Chaina ta bangaren kimiya da fasaha ga kasar China. Don haka Huawei na da matukar mahimmanci a gareta. Yanzu a fili take Amirka na bi duk inda karfin kamfanin ya kai domin kassara wannan nasara da Huawei ta samu".

Donald Trump, Xi Jinping
Hoto: picture alliance/AP Photo/ S. Walsh

Sai dai a yanzu rikicin Amirka da Chaina ya yi matukar zafafa ne, domin duniya ba ta yi sa'a ba aka samu shugabannin da ba sa sassauci, yayin da Trump ya zama mai yin abin da zuciyarsa ta raya masa, haka shi ma takwaransa na Chaina ba kanwar lasa ba ne, in ji Sebastian Heilmann:

"Mun samu manyan matsaloli biyu daga bangaren shugabanci, dukkan shugabannin suna amfani da tsarin kishin kasa. Na daya shi ne mutumin da komai ke a hannunsa wato Xi Jinping, na daya gefen kuma Donald Trump wanda ke fuskantar matsin lamba. Kuma dukkan wadannan shugabannin kowa baya son yin sassuci, ko da a ce dayansu ya mika kai. Wannan shi ne mummunan yanayi na shugabanci da yanzu ke kunna rikici tsakanin Amirka da Chaina"

Babban abin da ya fi kawo ta da jijiyar wuya dai shi ne batun fasahar zamani inda kasashen biyu ke tsere tsakaninsu, musamman batun karfin fasahar zamani da aka sani da G5. Wanda duk ya riga ya malaki wannan fahasar to kuwa shi ne zai rika iko da tattalin arzikin duniya. Wato dai a yanzu an game batun tattalin arziki da karfin soja waje dguda. Wanda kuma ke zama abun nuna karfi tsakanin kasashen biyu da suka fi kowace kasa ci-gaban fasahar zamani.