1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon yunkurin zaman lafiya a Sudan ta Kudu

Suleiman Babayo
December 22, 2017

Ana sabon yunkurin samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu tsakanin gwamnati da kungiyoyin 'yan tawaye, abin da zai taimaka wajen samar da agajin jinkai ga mutanen da suka tagayyara.

https://p.dw.com/p/2po2R
Äthiopien Friedensgespräche Süd Sudan
Hoto: picture alliance/dpa/abacaM. W. Hailu

Gwamnatin Sudan ta Kudu da wasu kungiyoyin 'yan tawaye sun saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a wannan Alhamis da ta gabata, a wani sabon yunkurin na samar da zaman lafiya a wannan kasa da ke fuskantar yakin basasa tun kimanin shekaru hudu da suka gabata, lamarin ya janyo tabarbarewar harkokin rayuwa ga fararen hula.

Tsagaita wutar zai kasance karkashin yarjejeniyar da aka kulla a shekara ta 2015, abin da ake gani zai iya taimakon ma'aikatan jinkai samun kai wa ga fararen hula wadanda suka tagaiyara. Yakin basasan na Sudan ta Kudu ya kai ga mutuwar dubban mutane, yayin da wasu kimanin milyan 12 suka tsere daga gidajensu.

Sudan ta Kudu ta fada cikin rikici a shekara ta 2013 lokacin da Shugaba Salva Kiir ya fatattaki tsohon mataimakinsa Riek Machar daga bakin aiki.