1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar barazanar tsaro a Somaliya

November 11, 2017

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa reshen kungiyar IS da ke kasar Somaliya ya sami karin mayaka da masu daukar nauyin ta'addanci daga kasashen Syria da kuma Iraki.

https://p.dw.com/p/2nRmE
Somalia Al-Shabaab Kämpfer
Hoto: picture alliance/AP Photo/F. A. Warsameh

Wani rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar kan kasar Somaliya, na nunin cewa reshen kungiyar IS da ke kasar ya sami karin mayaka akalla 200 kuma yana samun kudade daga kasashen Syria da kuma Iraki. A baya dai mayakan gwamnati da ke sami tallafin Amirka sun fatattaki mayakan kungiyar daga tungarsu da ke yankin Bari, sai dai duk da hakan bai hana su kaddamr da hare-hare ba.

Rahoton na majalisar Dinkin Duniya, ya kuma nuna damuwa kan yiwuwar yankin na Bari ya kasance dandalin sheke ayar mayakan da za su iya tudadowa daga ketaren Somaliyar musamman wadanda ake fatattaka daga kasashen Iraki da Syria. Wasu rahotannin na cewa a wannan Juma'a, dakarun Amirka sun kashe mayakan tarzoma da dama, a wani harin da suka kai a yammacin Mogadishu babban birnin kasar.