150413 Internet Afrika
April 18, 2013Kamfanin Google ya kaddamar da wannan saban tsari a Afirka ta Kudu.
Duk da cewar amfani da kafar sadarwa ta yanar gizo kokuma Internet ta zama ruwan dare gama duniya, amma a sassa da dama na Afirka da ma sauran kasashen masu tasowa na duniya,har yanzu miliyoyin jama'a a ba su wadata ba da wannan kafa.
Babban burin da Google ya ke bukatar cimma shine na rage gibi ta hanyar sadarawa tsakanin kasashe masu cigaban masana'antu da masu tasowa.
Fortune Sibanda jami'i a kamfanin Google reshen Afirka ta Kudu ya karin baiyani game da wannan husa'a:
"Wannan sabuwar husa'a ta na amfani da talbajan domin samar da Intanet.Bukatar itace mu bada tallafi wajen wadata jama'a ta hanyar yin amfani da yanar gizo ba tare da samun kuste ba, ko kuma illa ga hanyoyin da aka saba da su wajen shiga Intanet".
To saidai akwai bukatar wayar da kan jama'a game da hanyoyin yin amfani da wannan na'ura saboda haka Sibanda ya ce tuni sun fara fadakar da jama'a, ya kuma bayana dubarun da su ke amfani da su wajen jona yanar gizo da talbajan din :
"Yadda mu ke yi shine muna kafa na'urorin Recever wadda ta hanyarta ta sauti ke shigowa da kuma na'urar transmiter mai watsa sauti a wasu yankunan da muka riga muka tantance.
Duk talbajan da ke cikin wannan yanki za ta iya kamo na'urar Intanet.Mun fara kaddamar da shirin a birnin Cap Town".
Wannan husa'a ta kamfanin Google ta samu karbuwa daga kungiyoyi daban-daban na Afirka ta Kudu, sannan ta samu hadin kai daga masana ta fannin ilimin sadarawa.Tuni har an jona makarantu 10 a wannan kafa, Fortune Sabinda ya nuna mahimmancin daukar wannan mataki a kasashen Afirka:
"Wannan dubara na da baban tasiri mussamman a kasashen Afika,ta la'akari da matsalolin da ake fama da su ta hanyar yin amfani da Intanet.Sannan wani abun alfahari kyauta ne ake jona wa mutum Intanet ba tare da sisin kwabo ba, illa kawai mutum ya mallaki talbajan a gidansa a shagonsa kokuma aofis dinsa."
A halin yanzu kamfanin Google ya fara gwada husa'ar a kasar Afrika ta Kudu amma zai yada ta zuwa sauran kasashe Afirka a nan gaba.
Mawallafa: Herrler Andreas/ Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe