1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Tsugune ba ta kare ba

Ramatu Garba Baba
December 13, 2021

Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai saka kwalla wajen tarwatsa daruruwan masu zanga-zanga da suka mamaye fadar shugaban kasar da ke a Khartoum.

https://p.dw.com/p/44CDk
Sudan | Proteste in Khartoum
Hoto: Mahmoud Hjaj/AA/picture alliance

Ga dukkan alamu, tsugune ba ta kare ba a rikicin siyasan kasar Sudan, inda masu bore ke ci gaba da nuna adawa da gwamnatin da suka ce, sojoji ke jan ragamarta a fakaice, duk kuwa da mika mulki hannun Firaiminista Abdallah Hamdok da janar Abdel Fattah al-Burhan da ya jagoranci juyin mulkin yayi. 

Bukatar masu boren su ga an mika ragamar mulki kaco-kam a hannun farar hula ba tare da yin raba daidai da sojoji ba, sai dai ga dukkan alamu, abin kamar da wuya ganin jajircewar masu zanga-zangar da kuma cijewar sojojin da ke cikin gwamnatin wucin gadin. A karshen watan Nuwamban da ya gabata aka cimma wata yarjejeniya da bangaren farar hula dana sojojin kafin mayar da Hamdok kan karagar mulki.