Saduwa tsakanin Ministan tsaro na Isra'ila da Friministan Palesɗinu
July 5, 2010Talla
Ministan tsaro na ƙasar Isra'ila Ehud Barak ya gana da Firiministan Palesɗinu Salam Fayyad a birnin ƙudus.
Barak da Fayyad sun tattauna ne akan shinge zirin Gaza wanda hukumomin ƙasar ta Isra'ila suka yi sasauci akan sa a ƙwanakin baya bayan nan da kuma maganar tsaro da tattalin arziki.
A taron manema labarai da ya yi a Ramallah, bayan ganawar Firiministan na Palesɗinu ya shaida cewar tattaunar ta yi armashi sosai, kuma ya ce ya jaddada buƙatar ganin an kawo ƙarshen mulkin mallakar da Isra'ila ta ke yiwa Palesɗinu:
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Yahuza sadissu Madobi