Sakamakon wucin gadi na zaɓen Angola
September 3, 2012Kafofin yaɗa labaran ƙasar Angola sun bayyana shugaba Jose Eduardo dos Santos a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar a zaɓukan ranar Jumma'ar da ta gabata, tun ma gabannin kammala ƙidaya ƙuri'un da aka ka'ɗa, yayin da 'yan adawa kuma ke cewar an tafka maguɗi a zaɓen.
Jaridar Journal de Angola dake goyon bayan manufofin gwamnatin ƙasar Angola ta wallafa - a shafinta na farko- kan labarin da ke cewar "Gagarumar nasara ga jam'iyyar MPLA" tare da liƙa hoton shugaba Dos Santos yana tafa hannun sa, inda kuma labarin ya ci gaba da cewar dukkan alamu na nuni da cewar jam'iyyar ce ta yi nasarar lashe fiye da kaso 75 cikin 100 na ɗaukacin ƙuri'un da aka jefa.
Jaridar dai ta bayyana hakan ne bayan da hukumar zaɓen - ta bakin kakakinta Julia Ferreira ta sanar da sakamakon zaɓen na wucin gadi:
Ta ce " Bayan ƙidaya kaso 85 cikin 100 na ɗaukacin ƙuri'un da aka jefa jam'iyyar MPLA da ke mulki ce ta sami nasarar lashe kimanin kaso 73 cikin 100 na ɗaukacin ƙuri'un, yayin da jam'iyyar UNITA kuwa ta sami kimanin kaso 18 cikin 100."
Matsayin 'yan adawa ga sakamakon zaɓen Angola
Ko da shike hukumomin tsaro a ƙasar ta Angola sun kwatanta zaɓen da cewar ya gudana cikin zaman lafiya da walwala dai, amma kusan ɗaukacin jam'iyyun adawar ƙasar ne suka yi kakkausar suka ga zaɓen, da ma sakamakon da hukumar zaɓen ƙasar ta Angola ta sanar a wannan Lahadin, suna masu cewar da kamata yayi kafofin yaɗa labaran gwamnati su dakata tukuna - har sai hukumar zaɓen ta sanar da ɗaukacin sakamakon gabannin ayyana wanda ya yi nasara. Alcide Sakala, shi ne kakakin babbar jam'iyyar adawa ta UNITA, kuma ya mayar da martani ga wata sanarwar da tashar rediyon gwamnatin Angola ta fitar dangane da zaɓen :
Ya ce " Babu wani lokacin da UNITA ta fito fili ta yi na'am da sakamakon wucin gadi na zaɓen da hukumar zaɓen ƙasar Angola ta fitar. Muna son mu bayyana cewar ƙwarya-ƙwaryar sakamako ne hukumar ta fitar, wanda kuma tilas ne sai ya sami amincewar masu sanya ido da kuma jam'iyyun adawa."
Masu sanya ido na ƙetare sun yi na'am da zaɓen Angola
Tuni dai masu sanya ido na ƙasa da ƙasa suka bayyana ingancin zaɓen na Angola, kamar yanda Pedro Verona Pires daya jagoranci tawagar ƙungiyar tarayyar Afirka ya sanar, kana ita ma ƙungiyar ƙasashen da ke magana da harshen Portugues, dama ƙungiyar ci gaban ƙasashen yankin kudancin Afirka wadda aka fi sani da suna SADC suka bi sahu wajen yin na'am da sahihancin zaɓen, amma shugaban tawagar ta AU ya buƙaci hukumomin Angola da su inganta tsarin tantance masu sanya ido akan zaɓen kama daga na ƙetare har ya zuwa na cikin gida da ma na jam'iyyun siyasa. Sai dai kuma shugaban jam'iyyar PRS Eduardo Kuangana, ya ce akwai abin dubawa game da sakamakon:
Ya ce" Ban daɗe da sanar da cewar alal misali akwai wakilin mu da aka lakaɗawa duka a lardin Bengo, tare da tilasta masa tserewa ba. Abin taƙaici kuma shi ne cewar haka lamarin ya ke a wasu yankuna irin su Camama dake lardin Luanda. Hakan yana damuna sosai kuma ina ganin ba za mu amince da sakamakon zaɓen ba."
A yayin da ake dakon sakamakon ƙarshe na zaɓen ƙasar Angola a wannan Talatar, babu wanda ke tababar cewar shugaba Jose Eduardo dos Santos, ɗan shekaru 70 a duniya ne zai sake samun wa'adin shugabanci na shekaru biyar, kasancewar gyaran da aka yiwa tsarin mulkin ƙasar a shekara ta 2010 ya tanadi cewar shugaban jam'iyyar da ke da rinjaye a majalisar dokoki ne zai jagoranci ƙasar.
Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita : Abdullahi Tanko Bala