1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon yaki da ta'addanci a Masar

Salissou BoukariMarch 1, 2015

Rundunar sojan kasar Masar ta sanar cewa ta kashe a kalla 'yan jihadi 172 sakamakon wasu jerin matakai da ta dauka kan 'yan ta'addan a yankin Sinai.

https://p.dw.com/p/1EjYS
Hoto: Mohamed El-Shahed/AFP/Getty Images

Rundunar sojan kasar ta Masar ta yi wannan aiki ne tare da hadin gwiwar rundunar 'yan sandar kasar a watan da ya gabata na Febrairu a yankin Sinai, yankin da ke fuskantar hare-haren 'yan ta'adda babu kakautawa a kan jami'an tsaron kasar. Tun dai da Shugaban kasar mai ci yanzu Abdel Fattah Al-Sissi ya saukar da zababben Ssugaban na wancan lokaci Mohamed Morsi a watan Yulin 2013, jami'an tsaron Masar suka dukufa wajen abun da suka kira yaki da 'yan ta'adda a yankin arewacin kasar, inda 'yan kungiyoyin jihadi suke da karfi.

Rundunar sojan kasar ta Masar ta ce farmakin da ta kai a biranen Al-Arich, da Zoueid da kuma Rafa da ke kusa da iyaka da Isra'ila da kuma Zirin Gaza na Falastinu, ya bada damar kama wadanda ake zargi da ayyukan ta'addanci a kalla 229 tare da lalata mabuyarsu 85.