1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Brazil

October 4, 2010

A ranar 31 ga watan Oktoba ne al'ummar Brazil za ta je zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa.

https://p.dw.com/p/PTZo
Dilma RousseffHoto: AP

'Yar takarar da shugaban ƙasar Brazil mai barin gado Inacio Lula da Silva ya zaɓa domin ta gaje shi, ta yi nasarar zama ta farko a sakamakon zaɓen ƙasar Brazil da ya gudana jiya Lahadi, amma ta gaza samun rinjayen da doka ta tanadar domin kaucewa zuwa zagaye na biyu na zaɓen.

Bayan ƙidayar kashi 98 cikin 100 na ƙuri'un da al'ummar Brazil suka jefa, sakamakon ya nunar da cewar, Dilma Rousseff, jigo a majalisar zartarwar ƙasar, ta sami kashi 47 cikin 100, a yayin da ɗan takarar adawa, kana tsohon gwamnan jihar Sao Paulo, Jose Serra kuwa ya sami kaso 33 cikin 100 na yawan ƙuri'un. Sakamakon dai ya gaza baiwa Rousseff rinjaye fiye da kashi 50 cikin 100,domin kaucewa gudanar da zagaye na biyu a ranar 31 ga watan Oktoba.

Sakamakon ƙuri'ar jin ra'ayin jama'ar da ya gudana a lokuta daban daban a baya dai sun yi hasashen cewar, Rousseff za ta sami tsakanin kashi 50 zuwa 52 na ƙuri'u a zaɓukan na ranar Lahadi. Lula, wanda shi ne ya fi shahara a ɗaukacin shugabannin ƙasar Brazil, zai bar muƙamin ne bayan gudanar da wa'adin shugabanci har sau biyu a jere kamar yadda tsarin mulkin ƙasar ya tanadar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Yahouza Sadisou