Sakamakon zaɓen yan majalisun dokoki
July 5, 2012Ƙawancen jam'iyyun siyasar da ke goyon bayan shugaban ƙasar Senegal Macky Sall sun samu gagarumar nasara a zaɓen yan majalisun dokokin da aka gudanar a ƙarshen makon jiya.
Sakamakon wucin gadi da hukumar zaɓen ta baiyana, ya nuna cewar ƙawancen jam'iyyun sun samu kujeru 119 cikin 150 da ake da su a majalisar.Da yake baiyana sakamakon shugaban hukumar Demba Kandji ya ce jam'iyar tsohon shugaban ƙasar ta PDS wato Abdullahi Wade; ta samu kujeru 12,sanan wani ɗan aware na jam'iyar da ya kafa tasa jam'iyar ya samu wakilai 4 ,kana kuma sauran kujeru guda 15 sun fada cikin hanu wasu sauran ƙananan jam'iyyun siyasar.Wannan rinjaye da ƙawance da ake kira da sunnan na Beno Bokk Yakar ya samu a majalisar,zai baiwa shugaba Macky Sall damar ƙaddamar da manufofin gwamnatin sa
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasiru Auwal